Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-15 20:07:06    
Hu Jintao ya gana da shugaban Zanzibar Amani Abeid Karume

cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao dake yin ziyara a kasar Tanzania ya gana da shugaban Zanzibar Amani Abeid Karume a ran 15 ga wata a birnin Dares Salaam.

Hu Jintao ya furta cewa, kasar Sin ta mai da kasar Tanzania a matsayin dauwamammiyar aminiyar yin hadin gwiwa. Sin za ta cigaba da ba da taimako ga kasar Zanzibar bisa karfinta, da kalubalantar manyan kamfannonin kasar Sin da su zuba jari a kasar Zanzibar, da kuma nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin Zanzibar ta yi wajen ingiza bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma da kyautata zaman rayuwar jama'a.

A nasa bangare kuma, Amani Abeid Karume ya nuna cewa, kasar Zanzibar ta dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin, ta nuna godiya ga tallafin da kasar Sin ta samar mata cikin dogon lokaci, kuma ta nuna yabo ga sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa, tana son ta yi amfani da sakamakon da kasar Sin ta samu don bunkasa tattalin arzikin kasar, ta yadda bangarorin biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ciniki da yawon shakatawa da kuma kafa manyan ayyukan yau da kullum da dai sauransu.(Lami)