Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 20:51:18    
Takaitaccen bayani kan kasar Mali

cri

Kasar Mali tana kudu da Hamadar Sahara a yammacin Afirka. Ta yi iyaka da Senegal da Mauritania ta yamma, da kasar Algeria ta arewa, da kasar Nijer ta gabas, da kasashen Guinea da Cote D'ivore da Burkina Faso ta kudu. Fadin kasar ya kai muraba'in kilomita miliyan daya da dubu 240. yawan mutanen kasar Mali ya kai miliyan 13 da dubu 520, mazauna fiye da kashi 70 cikin dari suna amfani da harshen Bambaranci, harshen gwamnatin kasar shi ne Faransanci. Mazauna masu bin addinin musulunci ya kai kashi 68 cikin dari, kuma masu bin addinin Gumaka ya kai kashi 30.5 cikin dari, mazauna masu bin addinin Kiristanci ya kai kashi 1.5 cikin kashi dari. A arewacin kasar, akwai yanayin zafi na hadama, kuma a tsakiyar da kuma kudancin kasar, akwai yanayin zafi na Savanna.

Babban birnin kasar Mali shi ne Bamako, shugaban kasar Mali shi ne Amadou Toumany Toure, a watan Mayu na shekarar 2002 ya ci zaben zama shugaban kasar, kuma a watan Mayu na shekarar 2007, ya sake cin zaben zama shugaban kasar, a watan Yuni na shekarar ya yi rantsuwar kama aiki.

A ran 25 ga watan Oktoba na shekarar 1960, kasar Mali ta kafa dangantakar diplomasiya tare da kasar Sin. A watan Yuni na shekarar 2004, shugaban kasar Amadou Toumany Toure ya kawo ziyara a kasar Sin.(Abubakar)