Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-15 21:16:39    
Kafofin watsa labarai na kasar Mauritius suna mai da hankali kan ziyarar Hu Jintao a kasar

cri
Daga ran 16 zuwa ran 17 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai yi ziyarar aiki a kasar Mauritius, wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya yi ziyara a kasar bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, shi ya sa ziyarar tana da muhimmiyar ma'ana.

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, manyan kafofin watsa labarai daban daban na kasar Mauritius sun watsa labarai kan ajandar ziyarar Hu Jintao a kasar da kuma jiran zuwan shugaba Hu da sassa daban daban na zamantakewar al'umma musamman ma sashen kasuwanci na kasar suka yi, kuma sun nuna cewa, ziyarar za ta bude wani sabon shafi wajen karfafa hadin gwiwa da aminci tsakanin Sin da Mauritius.

A ran 14 ga wata, Jaridar Le Mauricien ta buga wani bayanin da Xiong Shizhong, babban sakataren kungiyar sada zumunci tsakanin kasashen Mauritius da Sin ya rubuta, inda ya bayyana cewa, bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1972, dangantakar ta samu babban ci gaba a fannoni daban daban. Tabbas ne ziyarar Hu Jintao a wannan karo za ta inganta hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya.(Kande Gao)