Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-10 21:23:35    
Shugaba Hu Jintao ya sauka kasar Saudiyya

cri

 

Bisa gayyatar da Abdullah Bin Abdul-Aziz, sarkin daular mulukiya ta Saudiyya ya yi masa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sauka birnin Riyadh, hedkwatar kasar a ran 10 ga wata da yamma, a gogon wurin, kuma ya fara ziyarar aiki a kasar Saudiyya. Wannan ya zama karo na biyu da shugaba Hu ya ziyarci kasar Saudiyya tun daga shekarar 2006.

Sarki Abdullah ya shirya bikin maraba da ziyarar Hu Jintao a filin jiragen sama.

A cikin jawabin da shugaba Hu Jintao ya bayar a filin jirgin sama, ya yaba da bunkasuwar dangantakar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasar Saudiyya ta samu sosai. Ya bayyana cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Saudiyya, kuma tana son yin kokari tare da kasar Saudiyya, don zurfafa hadin gwiwar da kasashen biyu suka yi, da kuma kawo moriya ga jama'ar kasashen biyu. Shugaba Hu Jintao ya ce, ana iya cewa, sabo da kokarin da bangarorin biyu suka yi, tabbas ne za a iya cimma nasarar yin wannan ziyarar, kuma dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da Saudiyya za ta iya samun bunkasuwa sosai. (Zubairu)