A ran 16 ga wata a birnin Dares Salaam na kasar Tanzania, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarci taron maraba da aka shirya masa, kuma ya ba da muhimmin jawabi kan tangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika.
A cikin jawabin, shugaba Hu Jintao ya yi nuni da cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta ci jarawabar sauye-sauyen halin da kasashen duniya ke ciki. A lokacin da da na yanzu, da kuma nan gaba, jama'ar Sin suna ba da muhimmanci kan zumuncin dake tsakaninsu da na Afrika, kuma suna mai da jama'ar Afrika a matsayin abokan da ake iya yin imani da dorawa a duk fannoni, kana za su zama abokai har abada.
Shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, kasashe masu ci gaba suna fi shan mawuyacin hali yayin da suke fama da matsalar kudi ta kasashen duniya. Amma a cikin mawuyacin hali, dole ne Sin da kasashen Afrika su taimakawa juna da hadin gwiwa don tinkarar matsalar kudi tare.
Bugu da kari, Hu Jintao ya ce, kasar Sin tana son hadin kai da kasashen Afrika a fannoni guda shida.(Asabe)
|