Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 19:20:57    
Takaitaccen bayani kan kasar Tanzania

cri

Hadaddiyar Jamhuriyar Tanzania na kunshi da yankuna 2, wato su babban yankin Tanganyika da tsibirin Zanzibar. Fadin kasar ya kai murabba'in kilomita dubu 945 da wani abu, ciki ya hada da fadin tsibirin Zanzibar na kilomita 2657.

Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2004, yawan jama'ar kasar ya kai fiye da miliyan 37, ciki har da mutanen tsibirin Zanzibar na kimanin miliyan 1. Jama'ar kasar na kasancewa cikin kabilu 126. Yaren kasar shi ne harshen Kiswahili, kuma shi da harshen Ingilishi, an mai da su harsunan gwamnatin kasar. Mafi yawan mazauna babban yankin Tanganyika na bin addinan Katolika, da Kirista, da kuma Musulunci, yayin da daukacin mazauna Zanzibar ke bin Islama.

Hedikwatar kasar ita ce Dares Salaam, wadda ke da yawan jama'a miliyan 3 a shekarar 2004. Matsakaicin yanayin zafin kasar shi ne digiri sentigired 25.8. Haka kuma, yanzu ana gina wata sabuwar hedikwatar kasar a Dodoma, inda jama'a miliyan 1.7 suke zaune, bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2002.

Shugaban kasar Tanzania mai ci shi ne Jakaya Mrisho Kikwete, wanda ya yi rantsuwar kama aiki a watan Disamba na shekarar 2005, yana kuma da wa'adin aiki na shekaru 5.

Tanzania kasa ce da ke dogaro kan aikin gona, kayayyakin da ake nomawa a kasar sun hada da masara, da alkama, da shinkafa, da dawa, da gero, da doya, da dai sauransu. Manyan kayan amfanin gona na sayarwa da ake noma, sun hada da kofi, da auduga, da rama, da kanju, da kanumfari, da ganyen shayi, da ganyen taba, da dai makamantansu.

Ya kasance da albarkatun wuraren yawon shakatawa a kasar Tanzania. Tabkuna 3 na Victoria, da Tanganyika , da Malawi, wadanda suka fi girma a nahiyar Afirka, sun kasance a kan iyakar kasar. Kilimanjaro, tsauni ne mafi tsayi a Afirka, wanda tsayinsa daga leburin teku ya kai mita 5895, ya shahara a duk duniya. Sauran wuraren yawon shakatawa na kasar Tanzania sun hada da gandun daji kamar su dutse mai aman wuta na Ngorongoro, da babban kwazazzabo na gabashin Afirka, da kuma wasu wuraren tarihi da na al'adu, kamar su wurin mafarin dan Adam da ya fi dadewa a duniya, da wurin tarihi na zaman 'yan kasuwa Larabawa da dai sauransu.

Kasar Sin ta kulla dangantakar diplomasiyya da Tanganyika a shekarar 1961, daga baya ta kulla hulda da Zanzibar a shekarar 1963. Bayan da Tanganyika ta hade da Zanzibar don zama kasa daya ta Tanzania, kasar Sin ta ci gaba da rike huldar diplomasiyya tsakaninta da su, kuma ta mai da ranar 26 ga watan Afrilu na shekarar 1964, a matsayin ranar kulla hulda a tsakanin kasar Sin da kasar Tanzania bayan da suka hade. Tun bayan da suka kulla huldar, kasashen 2 sun raya dangantakarsu ta hadin gwiwa da aminci a fannin siyasa da tattalin arziki lami lafiya, sa'an nan manyan shugabannin kasashen 2 su kan kai wa juna ziyara. A karshen watan Mayu na shekarar 2004, Benjamin William Mkapa, shugaban Tanzania na lokacin, ya hallarci taron kau da talauci a duniya, kuma ya ziyarci kasar Sin. A watan Yuni na shekarar 2006, Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya kai ziyarar aiki a kasar Tanzania, inda kasashen 2 suka gabatar da hadaddiyar sanarwa. A watan Afrilu na shekarar 2008, shugaba Kikwate na kasar Tazania ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin.