Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-13 22:57:09    
Shugaban kasar Sin ya isa kasar Senegal

cri
Bisa goron gayyatar da takwaran aikinsa na kasar Senegal Abdoulaye Wade ya yi masa ne, a ranar 13 ga wata da tsakiyar rana, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sauka a Dakar, babban birnin kasar Senegal, inda ya soma ziyarar aiki a kasar. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a kasar Senegal.

Shugaba Abdoulaye Wade na Senegal ya isa filin saukar jiragen sama don tarbar Hu Jintao da 'yan rakiyarsa.

A cikin wani jawabin da ya gabatar a filin saukar jiragen sama, Hu Jintao ya nuna babban yabo ga cigaban huldodin kasashen Sin da Senegal mai sauri bayan da aka maido da dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu. Ya bayyana fatansa na yin musayar ra'ayoyi tare da shugaba Wade kan yadda za'a yi don daukaka cigaban dangantakar kasashen biyu, da dai sauran muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Hu Jintao ya kuma nuna cewa, ziyararsa a wannan gami za ta inganta dankon zumunci da amincewar juna a tsakanin kasashen Sin da Senegal, da karfafa hadin-gwiwarsu a fannoni daban-daban, ta yadda za'a ingiza huldodin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.(Murtala)