Ran 15 ga wata, a birnin Dares Salaam, hedkwatar kasar Tanzania, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa Jakaya Kikwete na Tanzania, inda suka tattauna yadda za a ci gaba da raya dangantakar aminci da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2.
Jami'an harkokin waje na kasar Sin sun yi karin bayanin cewa, shugabannin Sin da Tanzania sun yi musayar ra'ayoyinsu kan dangantaka a tsakanin kasashen 2 da aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da matsalar hada-hadar kudi da dai sauransu.
Shugabannin 2 za su kuma halarci bikin daddale takardar yin hadin gwiwa a tsakaninsu bayan shawarwarin.
Ran 14 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka Dares Salaam, hedkwatar Tanzania bayan da ya kammala ziyararsa a kasar Senegal. A yayin da ya sauka Tanzania, shugaba Hu ya yi jawabi a rubuce cewar, ya kai ziyara a Tanzania ne domin inganta amincewa da juna a tsakanin kasashen 2 da habaka yin hadin gwiwa da tsara shiri kan makoma da kuma sa kaimi kan raya dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Tanzania zuwa sabon mataki. (Tasallah)
|