Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-14 16:15:27    
Shawarwarin shugaban kasar Sin da takwaran aikinsa na kasar Senegal

cri
A ranar 13 ga wata, a Dakar, babban birnin kasar Senegal, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Senegal Abdoulaye Wade.

Hu Jintao ya bayyana cewa, bayan da aka maido da dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Senegal a shekara ta 2005, huldodin kasashen biyu na samun cigaba yadda ya kamata. Sin na fatan inganta hadin-gwiwa a tsakaninta da Senegal a fannoni daban-daban, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su kara cimma alfanu.

Hu Jintao ya kuma jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da aka tabbatar da su a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka, kuma ba za ta rage yawan tallafin da take baiwa kasashen Afirka ba sakamakon rikicin hada-hadar kudi. Kasar Sin na fatan kara yin mu'amala da cudanya tare da kasashen Afirka, ciki har da kasar Senegal, don haye wahalhalu kafada da kafada.

A nasa bangare kuma, shugaba Abdoulaye Wade na kasar Senegal ya nuna cewa, bayan da aka maido da dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Senegal, Sin ta cika dukkan alkawarin da ta dauka na tallafawa kasar Senegal. Senegal ta nuna gamsuwa sosai game da hadin-gwiwa a tsakaninta da kasar Sin. Kasashen Afirka sun godewa kasar Sin saboda babbar gudummawar da take bayarwa a fannin daukaka cigaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta nahiyar Afirka.(Murtala)