Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-13 20:59:29    
Shugaban kasar Sin ya tashi daga kasar Mali zuwa kasar Senegal

cri
A ranar 13 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kawo karshen ziyararsa a kasar Mali, sa'annan ya tashi daga Bamako, babban birnin kasar zuwa kasar Senegal, don cigaba da rangadinsa a kasashen Asiya da Afirka guda biyar.

Shugaban kasar Mali Amadou Toumany Toure, da muhimman jami'ai da dama na gwamnatin kasar, gami da jakadun kasashen ketare dake kasar sun je filin saukar jiragen sama don yin ban kwana da Hu Jintao da 'yan rakiyarsa, inda shugaba Amadou Toure ya shirya gagarumin bikin ban kwana ga shugaba Hu Jintao.

Wannan ne karo na farko da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kai ziyara a kasar Mali wacce take yammacin nahiyar Afirka. A ziyararsa ta kasa da tsawon awoyi 24, Hu Jintao ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na Mali, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya kan cigaba da raya huldodin kasashen biyu. A waje guda kuma, Hu Jintao ya halarci bikin kaddamar da aikin gina babbar gada ta uku da gwamnatin kasar Sin ke bada taimako wajen gina ta, da bikin bude cibiyar yaki da cutar zazzabin cizon sauro, inda Hu Jintao ya jinjinawa Sinawa masu aikin jiyya dake Mali.(Murtala)