Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-12 14:32:48    
Shugaba Hu Jintao ya tashi zuwa kasar Mali bayan da ya kammala ziyara a kasar Saudiyya

cri

A ran 12 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga birni Riyadh zuwa kasar Mali bayan da ya kammala ziyarar aiki a kasar Saudiyya, daga nan ya ci gaba da ziyararsa a kasashen 5 na Asiya da Afrika.

A ran 10 ga wata ne, shugaba Hu Jintao ya isa Saudiyya don yin ziyara. Lokacin da yake bakunci a Saudiyya, shugaba Hu Jintao ya yi tattaunawa da sarkin Saudiyya Abdullah Bin Abdul-Aziz, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya daya kan kara bunkasa dangantakar abokantaka a tsakaninsu daga duk fannoni, da na tinkarar matsalar kudi tare. A cikin tattaunawar, shugaba Hu Jintao ya ba da shawarwari guda shida wajen bunkasa dangantakar dake tsakaninsu, kuma bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi biyar na hadin kan makamashi, kiwon lafiya, binciken cututtuka, sufuri, da al'adu.

Ban da wannan kuma, Hu Jintao ya gana da Abdulrahman Al Attiyah, babban sakataren kwamitin hadin kan kasashen larabawa na yankin Gulf, inda suka cimma matsaya daya kan karfafa hadin kai a tsakanin Sin da mambobin kasashe na kwamitin.(Asabe)