A ranar 15 ga wata, yayin da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ke zantawa da manema labaru na gida da na waje a Dar-es-Salaam watau hedkwatar kasar Tanzania, ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da tabbatar da shirin tallafawa Afrika da aka tsara a gun taron koli na Beijing da kyau kuma cikin lokaci, don ingiza dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin Sin da Afrika gaba.
Mr. Hu ya jaddada cewa, wannan shi ne karo na 6 da ya kai ziyara a Afrika, haka kuma ya kasance karo na 2 da ya kai ziyara a nahiyar Afrika bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, babban makasudin ziyararsa a Afrika na wannan gami shi ne inganta zumunci tsakaninsu, da zurfafa hadin gwiwa da fuskantar kalubale da kuma neman samun bunkasuwa tare. A yayin ziyararsa, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao da takwarorinsu na kasashen Afrika sun yi musanyar ra'ayi a kan dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da suka fi jawo hankulansu, kana kuma sun cimma ra'ayi daya a fannoni da dama. Ya jaddada cewa, ko da yake, rikicin hada-hadar kudi na duniya ya haifar da babbar matsala ga bunkasuwar tattalin arziki na Sin da na Afrika, amma wannan ba zai kawo tasiri ga inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ba.
Ya bayyana cewa, "A matsayin wata amintacciyar abokiya ta kasashen Afrika, gwamnatin Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki na Afrika da kyautata zaman rayuwar jama'ar wurin, kuma Sin tana fatan inganta hadin gwiwa tare da kasashen Afrika don haye wahalhalun da ke gabansu, gwamnatin Sin za ta ci gaba da tabbatar da shirin tallafawa Afrika da aka tsara a lokacin taron koli na Beijing da kyau kuma cikin lokaci, don inganta hakikanin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika da ingiza dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin Sin da Afrika.
Yayin da aka tabo maganar makomar dangantakar da ke tsakanin Sin da Tanzania, Hu Jintao ya nuna cewa, Tanzania wata muhimmiyar kawa ce ta kasar Sin, A cikin shekaru 45 da suka gabata, bayan da aka kafa huldar diplomasiyya tsakaninsu, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta samu bunkasuwa sosai, kuma an sami babban sakamako wajen hadin gwiwa a dukkan fannoni tsakaninsu. Dangantakar da ke tsakanin Sin da Tanzania ta kasance abin koyi ga kasashe matasa da suke yin mu'amala da hadin gwiwa cikin sahihanci tsakaninsu. Yayin da ya yi shawarwari tare da shugabannin kasar Tanzania, bangarori biyu sun fuskanci alkiblar samun bunkasuwar dangantaka ta bangarorin biyu tsakaninsu a karkashin sabon yanayin da ake ciki yanzu.
Ya bayyana cewa, bangarorin biyu sun amince da inganta dankon zumunci na gargajiya tsakaninsu, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa tsakaninsu, da ingiza dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi, ya yi imani cewa, a karkashin iyakacin kokari daga gwamnatin kasashen biyu da jama'ar kasashen biyu, dangantakar da ke tsakanin Sin da Tanzania za ta samu makoma mai haske, haka kuma za ta iya kara kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.(Bako)
|