Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-17 18:23:01    
Shugaba Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Mauritius kuma ya yi shawarwari tare da firaministan kasar

cri

Ran 17 ga wata a Port Louis, shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Mauritius ya gana da shugaba Anerood Jugnauth na kasar, kuma ya yi shawarwari tare da Mr. Ramgoolam firaministan kasar.

Yayin da yake ganawa da Mr. Jugnauth, Mr. Hu Jintao ya nuna cewa, bangarorin biyu suna mai da hankulansu kan huldar da ke tsakaninsu, suna yin hadin gwiwa kan fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu, da ba da ilmi, da yawon shakatawa, kuma sun sami kyakkyawan sakamako. Ya jaddada cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Mauritius domin rika yin ziyarce-ziyarce a tsakanin manyan jami'ansu, da fadada hadin gwiwar aminci a fannoni daban daban, da rika tuntuba da yin musayar ra'ayoyi kan harkokin duniya, da tinkarar matsalar hada-hadar kudi ta duniya tare. Mr. Jugnauth ya godewa taimako na dogon lokaci da kasar Sin ta samar ga kasar Mauritius, kuma ya yi imani da cewa, ziyarar shugaba Hu Jintao za ta karfafa huldar amincin da ke tsakaninsu.

Yayin da yake yin shawarwari tare da firaminista Ramgoolam, Mr. Hu Jintao ya gabatar da shawarwari guda 5 don bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Mr. Ramgoolam ya yarda da shawarwarin da Mr. Hu Jintao ya gabatar, ya kuma jaddada cewa, kasar Mauritius tana son fadada hadin gwiwar da ke kawo moriyar juna kan fannoni daban daban tare da kasar Sin. Ya nuna cewa, kasar Sin tana tafiya da mtakan da ta gabatar yayin taron koli na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka yadda ya kamata, kasar Mauritius tana yabawa haka sosai. [Musa Guo]