Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-13 09:01:28    
Shugaba Hu Jintao ya yi tattaunawa da shugaban kasar Mali

cri

A ran 12 ga wata a birnin Bamako, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tattauna da shugaban kasar Mali Amadou Toumany Toure, don yin musanyar ra'ayoyinsu kan yadda za a kara bunkasa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

An yi tattaunawar bayan da shugaba Hu Jintao ya isa birnin Bamako. Kuma shugaba Hu Jintao ya halarci bikin maraba da shugaba Toure ya shirya masa.

Bisa tsarin da aka yi, bayan tattaunawar, shugabannin kasashen biyu za su halarci bikin rattaba hannu kan yarjeniyoyi na hadin kai dake tsakanin bangarorin biyu, da ganawa da manema labaru tare.

A cikin takardar jawabin da ya bayar a filin jirgin, shugaba Hu Jintao ya ce, yana fatan zai yi musanyar ra'ayoyi da shugaba Toure da sauran shugabannin kasar Mali a kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da batutuwa na kasashen duniya da na shiyya-shiyya dake jawo hankulansu. Kuma ya yi imanin cewa, bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi, za a cimma buri na wannan ziyara wato na inganta zumunci, da zurfafa hadin gwiwa, da tinkarar kalubale tare, da kuma samun ci gaba tare.(Asabe)