A ran 12 ga wata a birnin Bamako, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi tattaunawa da shugaban kasar Mali Amadou Toumany Toure. Hu Jintao ya bayyana cewa, kasar Sin za ta aiwatar da dukkan matakan tallafawa da aka tabbatar da su a gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da aka yi a Beijing, da yin duk kokarinsa na ci gaba da ba da tallafi ga kasashen Afrika, da cire ko rage yawan basussukan da suka ci, da kuma kara yin cinikayya da zuba jari da kasashen Afrika, kana da karfafa hadin kai a tsakaninsu.
Bugu da kari, Hu Jintao ya kimanta babban ci gaba da aka samu a kan dangantakar dake tsakaninsu, kuma ya ba da shawarwari guda hudu a kan wannan batu. Kuma ya jaddada cewa, munin tasirin da matsalar kudi ta kawo wa kasashen Afrika ya bayyana. Kasar Sin tana ba da muhimmanci kan jama'ar Afrika kan fama da wahalhala, tana son kara mu'amala da kasashen Afrika ciki har da Mali a fannin tinkarar matsalar kudi don taimakawa jama'ar Afrika.
Shugaba Amadou Toumany Toure ya bayyana cewa, jama'ar Mali suna mai da hankali sosai kan zumuncin dake tsakaninsu da jama'ar Sin, da nuna godiya ga taimakon da kasar Sin ta baiwa kasar Mali a cikin tsawon lokaci. Bangaren Mali zai ci gaba da hada kai da Sin, da kuma tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. (Asabe)
|