Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-19 18:29:04    
Ziyarar hadin gwiwa ta sada zumunci da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi a Asiya da Afrika ta sami sakamako mai kyau

cri
A ranar 18 ga wata, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya dawo nan birnin Beijing lafiya, bayan da ya kammala ziyarar aikinsa a kasashe biyar na Asiya da Afrika watau Saudiyya da Mali da Senegal da Tanzania da Mauritius. Manazarta suna ganin cewa, ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi na wannan gami ta sami sakamako mai kyau.

Kasar Saudiyya ita ce zango na farko a cikin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi na wannan gami. A gun ziyararsa, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao da Sarkin Abdullah Bin Abdul-Aziz sun cimma daidaito a kan karfafa dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu. Mataimakin direkta na ofishin nazarin aikin tsaro da manyan tsare-tsare na cibiyar nazarin dangantakar da ke tsakanin kasashen duniya ta zamani ta kasar Sin Gao Zugui ya bayyana cewa, ziyarar aiki da Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi na wannan gami za ta iya kara inganta dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu da ci gaba zurfafa hadin gwiwa daga dukkan fannoni tsakaninsu. Haka kuma ya ci gaba da bayyana cewa:

"Daga sakamakon da aka samu a gun ziyarar shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao a Afrika, bangarorin biyu sun daddale yarjejeniyoyi da dama kan hadin gwiwa tsakaninsu, a karkashin dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare da aka kafa tsakaninsu a shekarar 2006. "

Bayan da shugaban kasar Sin ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Saudiyya, ya ci gaba da ziyarar aikinsa a kasashen Mali da Senegal da Tanzania da Mauritius da ke nahiyar Afrika. Wannan shi ne karo na 6 da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a nahiyar Afrika. Kwararre Zhang Yongpeng a cibiyar nazarin kimiyya da zamantakewar al'umma ta kasar Sin a kan batun Afrika, ya bayyana cewa, ziyara da dama da shugaban kasar Sin ya yi a Afrika, ta nuna mana matsayin haikan da Sin ke tsayawa wajen bunkasuwar dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afrika.

"A shekarar 1999, yayin da Mr. Hu Jintao ya zama mataimakin shugaban kasar Sin, ya taba kai ziyara a kasashen Afrika. Sabo da haka, ya kai ziyara ga kasashen Afrika sau 6 a cikin shekaru 10 da suka gabata"

Yayin da ya kai ziyara a kasashen Afrika na wannan gami, sau da kafa, Mr. Hu ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da tabbatar da shirin ba da agaji ga Afrika kamar yadda aka tsara a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a shekarar 2006, don kara zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin Sin da Afrika. Zhang Yongpeng na ganin cewa, ziyarar aiki da Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi a Afrika na da ma'anar musamman tsakaninsu. Ya bayyana cewa:

"Bayan da aka yi taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a watan Nuwanba na shekarar 2006, mun gabatar da wani shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika cikin shekaru uku masu zuwa. Kuma shugaban kasar Sin Mr. Hu ya gabatar da matakai 8 wajen taimakawa Afrika."

A halin yanzu da ake ciki, game da mummunan tasirin da rikicin hada-hadar kudi ta duniya ke kawo, kasashe masu ci gaba da masana'antu na cikin halin kaka-nika-yi. A gun ziyarar aiki da Mr.Hu ya yi a Afrika, ya bayyana cewa, ya kamata Sin da Afrika su hada kai tare, kuma sun haye wahalhalu da ke gabanmu, ya ce, Sin za ta ci gaba ba da taimako ga kasashen Afrika daidai gwargwadon iyawarta. Zhang Yongpeng yana ganin cewa, lalle, Sin ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta wajen taimaka wa kasashen Afrika.(Bako)