Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-15 19:08:41    
Kafofin watsa labarai na kasar Mali sun darajanta ziyarar Hu Jintao a kasar

cri
Daga ran 12 zuwa ran 13 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi ziyarar aiki a kasar Mali. Kuma a 'yan kwanakin nan da suka gabata, kafofin watsa labarai na kasar Mali sun sa muhimmanci sosai kan wannan ziyarar Hu Jintao da kuma nuna yabo sosai kan ziyarar.

A ran 12 ga wata, Jaridar Bunkasuwa ta gwamnatin kasar Mali ta watsa labari kan ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi a kasar a kan shafinta na farko, haka kuma jaridar ta watsa labarai filla filla kan ziyarar Hu a ran 13 ga wata, kuma ta ruwaito shugaba Hu, cewar shekara mai zuwa shekara ce ta cikon shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Mali, wannan ya shaida cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta shiga wani sabon zamani wajen samun bunkasuwa.

A ran 13 ga wata kuma, jaridar 'yancin kai ta kasar Mali ta watsa labari, cewar gwamnatin kasar Mali da kuma jama'ar kasar sun yi marhabin zuwan shugaba Hu Jintao da hannu biyu biyu, kuma za a samu wata kyakkyawar makoma wajen raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Mali.(Kande Gao)