A ranar 14 ga wata da safe, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya kammala ziyarar aikinsa a karo na farko a kasar Senegal, kuma ya bar babban birnin Dakar watau hedkwatar kasar Senegal, kuma zai ci gaba da ziyarar aikinsa a kasashe 5 dake Asiya da Afrika.
A wannan rana, a birnin Dakar shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gana da shugaban majalisar dattijai Pape Diop da shugaban majalisar dokoki watau Mamadou Seck kuma sun yi musanyar ra'ayi kan dangantakar bangarori biyu da manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da suka mai da hankali sosai a kai.
Shugaban kasar Senegal Abdoulaye wade ya yi bikin ban kwana a babban filin jiragen sama na kasar.(Bako)
|