Ran 12 ga wata da yamma, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka birnin Bamako, hedkwatar kasar Mali, inda ya fara ziyarar aikin a karo na farko a wannan kasa da ke yammacin Afirka.
A cikin jawabin da ya bayar a rubuce, shugaba Hu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 49 da kasashen Sin da Mali suka kulla hulda a tsakaninsu, kasashen 2 sun yi ta raya zumunci a tsakaninsu, kana kuma sun sami sakamako da yawa sakamakon yin hadin gwiwa a fannoni daban daban. Kasar Sin na darajanta hulda a tsakaninta da kasar Mali, tana son gama kanta da Mali domin bude sabon shafi na yin hadin gwiwar abokantaka a tsakaninsu. Kazalika kuma, shugaba Hu ya nuna cewa, yana sa ran yin musayar ra'ayoyi tare da takwaransa na Mali Amadou Toumany Toure da sauran shugabannin Mali kan hulda a tsakanin kasashen 2 da al'amuran duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankalinsu duka. Ya yi imani da cewa, a karkashin kokarin da bangarorin 2 suke yi, tabbas ne ziyararsa za ta iya inganta zumunci da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 domin tinkarar kalubale tare da kuma samun bunkasuwa tare.
Shugaba Amadou Toumany Toure da wasu manyan jami'an gwamnatin Mali sun yi maraba da shugaba Hu da tawagar rakiyarsa a filin jirgin saman.(Tasallah)
|