Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-11 09:37:07    
Shugabannin kasashen Sin da Saudiyya sun cimma matsaya daya kan zurfafa dangantakar abokantaka tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni

cri

A ran 10 ga wata a birnin Riyadh, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi shawarwari da sarkin kasar Saudiyya, inda bangarorin biyu suka bayyana fatansu na zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni, da tinkarar matsalar kudi tare, da kuma kara mu'amala da daidaito a tsakaninsu a kan harkokin kasashen duniya da na yankuna, don daga huldar dake tsakanin bangarorin biyu zuwa sabon matsayi.

Shugaba Hu Jintao ya nuna cewa, yanzu dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta fi kyautata a tarihi. Bangaren Sin yana mai da hankali kan rawar da kasar Saudiyya ta taka a kan kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da tabbatar da tsaron makamashin kasashen duniya da dai sauransu, kuma ya ci gaba da ba da muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare. Halin da ake ciki a kasa da kasa yana canjawa, musamman dukkan kasashen biyu suna fuskantar kalubalen da matsalar kudi ke kawo wa. Sabo da haka, hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu yana da muhimmanci sosai.

Ban da wannan kuma, shugaba Hu Jintao ya ba da shawarwari guda shida a kan bunkasa dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu wajen ci gaba da kai wa juna ziyara tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, da kara hadin kan tattalin arziki da cinikayya, da kuma karfafa fahimtar juna da daidaito a kan manyan batutuwan kasashen duniya da na yankuna da dai sauransu.

Sarki Abdullah Bin Abdul-Aziz ya amince da kimantawar da shugaba Hu Jintao ya yi a kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da shawarwarin da ya gabatar. Ya bayyana cewa, kasar Sin ita ce ainihin abokiyar kasar Saudiyya. Bunkasa huldar abokantakar dake tsakaninsu zai dace da fa'idar bangarorin biyu, shi ya sa kasar Saudiya tana da fata sosai ga bunkasa dangantakar dake tsakaninsu. Kuma bangaren Saudiyya yana son hadin gwiwa da Sin a fannoni daban daban da musanya ra'ayoyinsu a kan manyan batutuwan kasashen duniya da na yankuna.

Shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, ya kamata kasashen biyu su karfafa daidaito a tsakaninsu don tinkarar matsalar kudi cikin hadin gwiwa. Kuma sarki Abdullah Bin Abdul-Aziz ya nuna amincewa da wannan batu.

Bayan shawarwarin, shugabanni biyu sun halarci bikin rattaba hannu kan yarjeniyoyi biyar na yin hadin gwiwa wajen makamashi, da kiwon lafiya, da binciken cututtuka, gami da tafiye-tafiye, da al'adu. (Asabe)