Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-13 10:05:52    
Kafofin watsa labaru na Saudiyya sun darajanta ziyarar Hu Jintao

cri
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyarar aiki a kasar Saudiyya tun daga ran 10 zuwa 12 ga wata. A kwanakin nan, manyan kafofin watsa labaru na kasar Saudiyya sun dora muhimmanci kan ziyarar Hu Jintao, kuma sun bayar da labarai da nuna yabo game da wannan lamari.

A ran 11 ga wata, jaridar Al Riyadh da aka fi bugawa a Saudiyya ta bayar da labari na game da ziyarar Hu Jintao tare da wani hoto a cikin shafi na farko. Kuma jaridar ta buga wani sharhin edita mai taken "Sin, abokiya ce", inda aka bayyana cewa, zumuncin dake tsakanin Saudiyya da Sin yana da dogon tarihi, an inganta dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu lami lafiya a cikin shekarun nan, kuma an yi imani cewa, za a kara hadin gwiwa tsakaninsu a nan gaba.

Jaridar Arab News ta kasar Saudiyya ta buda wani labari na game da shawarwari tsakanin sarkin Saudiyya Abdullah Ben Abdel Aziz da shugaban Sin Hu Jintao tare da wani hoto a cikin shafi na farko a ran 11 ga wata.

Jaridar Al Hayat ta buga wani labari na game da ziyarar Hu Jintao a ran 12 ga wata, inda ta jaddada cewa, kasashen Saudiyya da Sin sun samu bunkasuwa a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma na kimiyya da fasaha.(Zainab)