Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-17 23:23:08    
Shugaba Hu Jintao ya tashi daga kasar Mauritius bayan da ya kammala ziyararsa a kasar

cri

Ran 17 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya tashi daga birnin Port Louis domin dawo kasar Sin bayan da ya kammala ziyarar aiki ta farko a kasar Mauritius. Mr. Ramgoolam firaministan kasar Mauritius ya shirya biki a filin jirgin sama domin raka da Mr. Hu Jintao.

Yayin da yake yin ziyara a kasar Mauritius, bi da bi ne Mr. Hu Jintao ya gana da shugaba Anerood Jugnauth na kasar, kuma ya yi shawarwari tare da Mr. Ramgoolam firaministan kasar da shugaban jam'iyyar adawa. Bangarorin biyu sun yi shawarwari da yin musayar ra'ayoyi kan harkokin yankuna da duniya da ke jawo hankulansu. Ban da haka kuma sun sami ra'ayi iri daya wajen sa kaimi ga hadin gwiwar da ke moriyar juna tsakanin kasashen biyu. [Musa Guo]