Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-16 16:01:00    
Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya kammala ziyararsa a kasar Tanzania

cri

A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Tanzania a hukunce, kuma ya bar birnin Dar-es-Salaam kuma zai kai ziyara a kasar Mauritius, don ci gaba da ziyarar hadin gwiwa ta sada zumuncinsa a kasashen Asiya da Afrika.

Shugaban kasar Tanzania Jakaya Mrisho Kikwete ya yi kasaitaccen bikin ban kwana a babban filin jiragen sama na kasar. Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a kasar Tanzania. A lokacin ziyararsa, shugabannin Sin da Tanzania sun yi shawarwari, kuma sun cimma ra'ayi daya a kan inganta dankon zumunci na gargajiya tsakaninsu da zurfafa hakikanin hadin gwiwa da ingiza dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci tsakaninsu. Yayin da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi ziyara a birnin Dar-es-Salaam, kuma ya yi jawabi game da dangantakar tsakanin Sin da Afrika, inda ya jaddada cewa, jama'ar Sin sun dora muhimmannci sosai a kan dankon zumunci na gargajiya da ke kasancewar tsakanin Sin da Afrika, kuma ta mayar da jama'ar Afrika a matsayin kyawawan abokanta da take iya dogara, yana fatan jama'ar Sin da Afrika za su zama kyawawan abokai har abada.

Kasar Tanzania kasa ce ta hudu da shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao ya yi ziyarar hadin gwiwa ta sada zumunci a kasashen Asiya da Afrika, tuni dai, ya kai ziyara a kasashen Saudiyya da Mali da Senegal.(Bako)