Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-12 10:16:49    
Shugaba Hu Jintao ya gana da babban sakataren kwamitin hadin kan kasashen larabawa na yankin Gulf

cri

A ran 11 ga wata da yamma a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da Abdulrahman Al Attiyah, babban sakataren kwamitin hadin kan kasashen larabawa na yankin Gulf, inda bangarorin biyu suka kara cimma matsaya daya mai muhimmanci kan karfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kwamitin hadin kan kasashen larabawa na yankin Gulf.

Shugaba Hu Jintao ya ce, a 'yan shekarun baya, kwamitin hadin kan kasashen larabawa na yankin Gulf ya riga ya zama muhimmin abokin huldar kasar Sin wajen hadin kan tattalin arziki da cinikayya da na makamashi. Bangaren Sin yana fatan bangarorin biyu za su yunkura tare don kyautata tsarin hadin gwiwa.

Ban da wannan kuma, shugaba Hu Jintao ya ba da shawarwari guda hudu wajen kara bunkasa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Mista Attiyah ya nuna yarda da wadannan shawarwari sosai. Ya bayyana cewa, kwamitin hadin kan kasashen larabawa na yankin Gulf yana fatan za a zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, kuma yana fatan bangarorin biyu za su gaggauta gudanar da tsarin tattaunawa bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, kana su kyautata huldar dake tsakaninsu a duk fannoni.(Asabe)