Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 18:35:23    
Takaitaccen bayani kan cigaban dangantakar tsakanin Sin da Afirka

cri

Duk da cewa ya kasance da nisa tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka, amma aminci da hadin gwiwa a tsakanin bangarorin 2 na da dogon tarihi. Cikin rabin karnin da ya wuce, kasar Sin da kasashen Afirka sun jure kalubale da yawa, suna ta kyautata huldarsu ta aminci da hadin kai.

A watan Mayu na shekarar 1956, kasar Sin ta kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Masar, batun ya bude shafin kyautata dangantaka a tsakanin Sin da Afirka. A baya ga hakan, kasashen Afirka da suka samu 'yancin kai da dumi-dumi sun kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin daya bayan daya. Kawo yanzu, kasashe 49 cikin kasashe 53 na Afirka sun kulla dagantaka da kasar Sin. Kasar Sin da kasashen Afirka dukkansu na kan hanyar neman samun ci gaban masana'antu, a wajen harkar kasa da kasa kuma, dukkansu na kokarin lalubo adalci da damar nuna ra'ayinsu. Bangarorin 2 ba su taba rikici da juna kan babbar moriyarsu ba, haka kuma suna wa juna kallon girmamawa yayin da suke mu'amala. Sa'an nan a fannin siyasa, Sin da Afirka na mara wa juna baya, suna kuma taimakon juna da amfana wa juna a fannin tattalin arziki.

A yayin da ake kula da harkokin kasa da kasa, Sin da Afirka suna tausayawa juna, da tallafa wa juna. A shekarar 1971, kasar Sin ta sake samun wakilci a MDD bisa kuri'un da kasashe 76 suka jefa na nuna yarda, kuma kasashe 26 daga cikin su sun kasance kasashen Afirka. Daga shekarar 1971 zuwa shekarar 1978, tallafin da kasar Sin ta baiwa Afirka ya karu cikin sauri. A shekarar 1976 an gama aikin gina wani layin dogo da ya tashi daga kasar Tanzania zuwa kasar Zambia bisa taimakon kasar Sin, kuma layin nan mai tsawon kilomita 1800 an bayyana shi a matsayin wani aikin ishara cikin ayyukan tallafi da kasar Sin ta baiwa Afirka.

Tun daga shekarun 1980, dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta jure jarrabawar sauyin yaniyin siyasar duniya, ta ci gaba da samun inganci. A watan Mayu na shekarar 1996, Jiang Zemin, shugaban kasar Sin na lokacin ya kai ziyara ga nahiyar Afirka, inda ya gabatar da 'shawarwari 5 don kulla dangantakar hadin gwiwa mai dorewa a tsakanin Sin da Afirka yayin da ake shigowa cikin karni na 21', wato su "nuna aminci mai sahihanci, da kasancewa cikin zaman daidai wa daida, da kara hadin kai, da neman samun cigaba tare, da share fage domin samun makoma mai kyau", inda ta shawarwarin aka bude wani sabon shafi dangane da hulda mai kyau da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Zuwa karni na 21, duk bangaren Sin da na Afirka sun samu ra'ayin cewa, ya wajibi da a karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Watan Oktoba na shekarar 2000, an kira taron ministoci na farko na 'dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka' a birnin Beijing, hedikwatar kasar Sin, inda aka sanar da cewa, Sin da Afirka sun kuduri niyyar kulla sabuwar dangantaka, wadda za ta samu zaman karko mai dorewa, kuma za ta tabbatar da kasancewar bangarorin 2 daidai wa daida da amfana wa juna.

Gwamnatin kasar Sin ta fito da 'takardun munufar kasar sin kan Afirka' a watan Janairu na shekarar 2006, inda aka yi kira da kyautata huldar tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi, ta yadda za a tabbatar da sharadin daidai wa daida da yin imani da juna a fannin siyasa, da samun hadin gwiwa da amfana wa juna a fannin tattalin arziki, da kara yin mu'amala da koyawa juna al'adu. Kiran ya samu karbuwa sosai a cikin kasashen Afirka. A wajen taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a watan Nuwamba na shekarar 2006, shugabannin kasashen Afirka da na kasar Sin sun sa hannu kan yarjejeniyar taron kolin, da taswirar shimfida aiki ta Beijing ta shekarar 2007 zuwa ta 2009. Bayan samun takardun, kasar Sin da kasashen afirka sun yi hadin gwiwa da ya fi shafar fannoni da yawa da samar da amfani, inda aka kara sa lura kan hakikanin abubuwa. Ta haka, kasar Sin da kasahen Afirka sun samar da gudummawa ga gamayyar kasa da kasa a fannonin kiyaye zaman lafiya, da raya kasa, da kuma hadin gwiwa.

Shekarun baya, cinikayya a tsakanin Sin da Afirka na karuwa cikin sauri, ta yadda yawan kudin cinikayya ya kai dalar Amurka biliyan 106.8 a shekarar 2008. Har wa yau kuma, kayayyakin da kasashen Afirka ke fitarwa da suka hada da makamashi, da danyun kayayyaki, da kayan masana'antu, sun fara kwararawa cikin kasuwannin kasar Sin.

Cikin shekaru fiye da 50 a bayan da sabuwar kasar Sin ta kulla dangantaka da kasashen Afirka, kasar Sin ta ba da taimako ga kasashen Afirka wajen gina kayayyaki da gine-ginen more rayuwar jama'a fiye da 900, da kuma samar wa mutane kimanin dubu 20 da suka zo daga kasashen Afirka 50 da kudin tallafin karatu, da tura masu aikin likitanci dubu 16 zuwa kasahen Afirka 47, wadanda suka yi jiyyar mutane kimanin miliyan 180. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta daina karbar haraji kan kayayyakin da wasu kasashen Afirka masu fama da talauci ke sayar wa kasar Sin, don samar da yanayi mai sauki kan aikin fitar da kayyakin Afirka zuwa kasar Sin. Haka kuma, kasar Sin ta dauki matakai ta dauke nauyin da ke wuyan kasahen Afirka na biya bashi. Zuwa shekarar 2007, kasar Sin ta yafe wa kasashen Afirka bashin da yawansa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 10.9, haka kuma ta yi alkawarin yafe musu bashin fiye da Yuan biliyan 10 a nan gaba.

Bankin duniya ya yi bayanin a cikin rahotonsa na shekarar bara da cewa, tallafin da kasar Sin ke baiwa kasashen Afirka, ya sa kasashen Afirka da yawa suka samu babban cigaba a fannin gina kayan more rayuwa. Kasar Sin ta ba da gudummawa ga nahiyar Afirka kan aikinta na kawar da talauci. Shugabannin kasashen Afirka da yawa su ma sun nuna godiya a fili ga gwamnatin kasar Sin, kan taimakon da ta bayar cikin karimci kuma ba tare da ko wane sharadi ba. (Bello Wang)