Sharhi Ma'aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar Ebola mai tsanani 2014-08-26 Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta bayar da wani rahoto kan halin da ake ciki game da cutar nan mai matukar hadari ta Ebola, inda ta bayyana cewa, tun farkon barkewar cutar Ebola har zuwa yanzu, ma'aikatan kiwon lafiya 240 ne suka kamu da cutar, inda rabinsu suka mutu. WHO na ganin a wannan karo ma'aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar ta Ebola mai tsanani, wanda ba a taba ganin irinta a baya ba...
| Jama'ar Afirka suna da bambancin ra'ayi game da amfani da magungunan gwaji kan cutar Ebola 2014-08-20 A 'yan kwanakin baya, hukumar lafiya ta duniya WHO ta yarda da yin amfani da magungunan gwaji wajen shawo kan cutar Ebola, bayan haka kuma, kasashen Amurka da Canada da dai sauransu bi da bi suka baiwa kasashen na Afirka wadannan magunguna a karo na farko, amma jama'ar nahiyar Afirka sun nuna bambacin ra'ayi game da amfani da wadannan magunguna...
| Kungiyar SADC ta bukaci mambobinta da su mai da hankali kan rigakafin cutar Ebola 2014-08-19 An rufe taron shugabannin kungiyar raya yankin kasashen kudancin Afirka wato SADC karo na 34, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a birnin Victoria Falls da ke kasar Zimbabwe, inda kungiyar ta bukaci mambobinta da su mai da hankali kan rigakafin cutar Ebola, a karshen taron mambobin kungiyar sun cimma ra'ayi guda don ganin wannan yanki ya kasance tamkar tsintsiya madaurin ki daya...
| Yadda za ka wanke hannunka domin yaki da cutar Ebola 2014-08-15 Idan har ba ka wanke hannunka yadda ya kamata ba sannan ka taba fuskarka ko wuraren da jama'a ke amfani da su, hakika kana iya kamuwa da kwayoyin cuta har ma ka yada wa wasu kamar cutar zawo da mura, dukkansu ana yada su ne idan mutum ya taba hannun wani...
| Likitocin kasar Sin sun hada kai da 'yan uwansu na Afirka wajen yaki da cutar Ebola 2014-08-15 A halin yanzu dai cutar Ebola tana kalubalantar kasashe da dama na yammacin Afirka, cutar da ta fi tsanani a tarihi tun bayan shekarar 1976 da aka fara ganon cutar Ebola, ya zuwa yanzu cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu. Game da bazuwar cutar Ebola, likitocin kasar Sin sun ci gaba da aiki tare da 'yan uwansu na Saliyo, kasar da ta fi shan wahalar cutar Ebola...
| |
|