A yankin yammacin Afirka inda cutar ta Ebola tafi tsananta, tarayyar Nijeriya ta zama kasa ta uku da ta sanar da kafa dokar ta baci, bayan kasashen Saliyo da Liberia.
A daya bangaren kuma mahukuntan kasar Saliyo sun tura sojoji da 'yan sanda kimanin 1500 zuwa yankunan da ake killace wadanda suka kamu da cutar a gabashin kasar.
Kaza lika kasar Mauritania, da Guinea Bissau, da sauran kasashen yammacin Afirka su ma na tsananta bincike a kan iyakokinsu, domin hana cutar ta Ebola shiga kasashensu. Bugu da kari, da dama daga kasashen Afirka na daukar matakan kandagarkin yaduwar wannan cuta.
Bisa labaran da kafofin watsa labarun kasar Chadi suka bayar, an ce gwamnatin kasar ta dakatar da dukkan jiragen sama daga Najeriya sauka a kasar. Kana ministan ma'aikatar lafiya na kasar Zambia Emmanuel G. Kasonde, ya bayyana cewa an dakatar da shigar dukkanin mutanen dake daga kasashe masu fama da cutar ta Ebola shiga kasar, za kuma a rika gudanar da binciken lafiyar jama'ar kasar masu komawa gida daga kasashen da aka samu bullar cutar.
Filin jiragen sama na Jomo Kenyatta dake kasar Kenya, na matsayin wata babbar tasha ga fasinjojin kasashen yammacin Afirka, kuma kasar Kenya ta bayyana cewa, ba za a dakatar da zirga-zirgar jirage zuwa kasar Guinea, da sauran kasashe masu fama da cutar Ebola ba, sai dai kawai tilas ne a binciki fasinjojin da suka taso daga wadannan kasashe.
Bugu da kari, a cewar kamfanin dillancin labaru na kasar Senegal, an gano wani mutum guda da ake zargin ya kamu da cutar Ebola a birnin Ourossogui dake arewacin kasar, tuni kuma aka killace shi a wani asibitin yankin.
Wannan ne dai karon farko da aka gano wani mutum da aka zaton yana dauke da cutar Ebola a kasar ta Senegal a wannan lokaci. (Zainab)