in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu sabbin wadansu da suka kamu da Ebola a Najeriya
2014-08-22 20:43:41 cri
An samu sabbin bayanai na wadansu mutane 2 da suka kamu da cutar Ebola a Najeriya,inda cutar yanzu haka ta hallaka mutane 5 inji ministan kiwon lafiya Onyebuchi Chukwu ranar jumma'an nan.

Jami'in na Najeriya yace sabbin wadanda suka kamu da cutar iyalan jami'an kiwon lafiyan nan ne da suka duba Patrick Sawyer Dan asalin kasar Liberiya da ya fara shigowa da cutar a kasar.

Wadannan sabbin kamun na ebola an masu gwajin da ya nuna suna dauke da kwayar cutar kamar yadda Mr Chukwu yayi ma manema labarai bayani a Abuja babban birnin tarayyar kasar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China