Pereire ya ce gwamnatin Guinea Bissau, ta yanke hukuncin rufe bangaren kudanci da gabashin kan iyakar kasarta da Guinea, saboda wannan ita ce hanya mafi inganci, da zata haramta yaduwar cutar a kasarsa.
Hukumar lafiya ta duniya tace kawo yanzu barkewar cutar ta Ebola yayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu daya a kasashen Africa ta yamma tun daga farkon wannan shekarar da muke ciki.( Suwaiba)