in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya alkawarta dakile cutar Ebola
2014-08-12 10:05:10 cri

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ce gwamnatinsa na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin dakile yaduwar cutar nan mai saurin kisa ta Ebola.

Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani, da wata kungiya mai zaman kanta ta shirya a Abuja fadar mulkin kasar, ya kara da cewa zai gana da daukacin gwamnonin kasar 36 da kwamishinonin kiwon lafiya a ranar Laraba, domin tabbatar da ana daukar matakan hana yaduwar wannan annoba a dukkanin sassan kasar.

Daga nan sai ya yi fatan daukacin masu ruwa da tsaki, kamar malaman addinai za su ci gaba da wayar da kan mabiyansu, game da hanyoyin kaucewa yada cutar.

A Jumma'ar da ta gabata ne dai fadar shugaban Najeriyar ta sanar da ware tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 11.6, domin yaki da yaduwar wannan cuta ta Ebola.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China