Sanarwar ta ce, bisa la'akari da yadda cutar Ebola ta zama babbar matsalar dake adabar duniya, kasar Senegal ta tsaida kudurin sake rufe kan iyakar kasarta da kasar Guinea. Ban da wannan kuma, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Senegal ta tsaida hana shigowar jiragen sama da jiragen ruwa daga kasashen Guinea, Saliyo da Liberia zuwa kasar Senegal.
A watan Maris din shekarar bana ne dai, kasar Senegal ta sanar da rufe iyakar kasa a tsakaninta da kasar Guinea dake fama da cutar Ebola, amma kuma aka bude iyakar a watan Mayu. Ya zuwa yanzu, babu wani mutumin kasar Senegal da ya kamu da cutar Ebola.(Zainab)