Wani jami'in gudanarwa na MDD a kan daukar matakan dakile cutar Ebola Dr. David Naborro, wanda kuma shi ne ya jagoranci wata tawaga MDD zuwa Afrika ta yamma ya ce, barkewar cutar, idan aka kwatanta da shekarun baya, a yanzu ta fi kama jama'a da yawa, kuma tana ci gaba da yaduwa.
Dr. Naborro wanda yake jawabi ga manema labarai ya ce, idan har ana so a kawar da cutar, akwai bukatar daukar muhimman matakai daga bangarori dabam dabam na al'umma, da kuma kungiyoyin MDD, gami da kungiyoyin kare hakkin bil'adama da kasashen duniya baki daya.
Hakazalika mataimakin babban darektan hukumar lafiya ta duniya, wanda shi ma na cikin tawagar da ta ziyarci Afrika ta yamma Dr. Keiji Fukuda, ya ce, cutar Ebola tana da kalubale, domin dole a daura yakin murkushe cutar tun da ba wai matsala ba ce kawai da ta addabi kasar Saliyo, matsala ce da ta shafi duniya baki daya.
Dr. Keiji ya yi fatan za'a iya shawo kan cutar cikin watanni 6. (Suwaiba)