Wani ma'aikacin kiwon lafiya, 'dan Ingila dake zaune a kasar Saliyo wanda aka gano yana dauke da cutar Ebola, an mai da shi gida a birnin Landan, kamar yadda mahukuntar Ingila suka sanar a ranar Lahadi.
Sashin kiwon lafiya ya tabbatar da cewa, sakamakon shawarar bangaren kiwon lafiya, an cimma matsaya na komawa da mara lafiyar nan, 'dan Ingila zuwa gida wanda yanzu haka ba ya jin dadin jikinsa, amma bai yi tsanani ba.
Mara lafiyan, an dauke shi ne a jirgin musamman da aka mashi tanadin mai suna C17 na sojin sama zuwa filin saukan jiragen saman Northolt na sojin sama, in ji wata sanarwa.
Kafofin watsa labarai na kasar sun ba da labarin cewa, mara lafiyar da shekaru 29 da haihuwa, da ake kyautata zaton ma'aikacin jinya ne wato nas, William ya kamu da cutar ne lokacin da yake duba sauran marasa lafiya a wani asibiti da yanzu haka ma'aikatan kiwon lafiya nas 15 suka rasu daga cutar.
Ya zuwa 20 ga wannan watan da muke ciki, adadin wadanda suka kamu da cutar a kasashen Liberiya, Guinea, Saliyo da ma Nigeriya sun kai 2,615 da suka hada da 1,427 da suka mutu. (Fatimah)