Ma'aikatar lafiyar wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, ta kara da cewa yanzu haka ana dakon sakamakon gwajin da aka yiwa maras lafiyan.
An dai ce mutumin dalibi ne a fannin aikin likita daga wata kasa ta Turai, shi ne kuma mutum na farko da ake ganin mai yiwuwa ya kamu da wannan cuta ta Ebola a kasar ta Rwanda, tun bullarta a wasu kasashen dake yammacin Afirka.
Gwamnatin kasar dai ta bukaci al'umma da su kwantar da hankulansu, su kuma kara kulawa, yayin da ma'aikatar lafiyar kasar ke ci gaba da daukar matakan hana barkewar cutar a kasar. (Saminu Alhassan)