Ministan lafiya na jamhuriyar damokradiyyar Congo DRC Felix Kabange Numbi ya bayyana cewar, wasu mutane biyu sun mutu a sakamakon cutar Ebola a garin Djera, wanda ke yankin arewa maso yammacin gundumar Equateur na kasar da ke yankin tsakiyar Afrika.
A yayin da ministan ke jawabi ta kafar gidan talabijin na kasar, ya kara da cewa, a wannan watan na Agusta, an samu barkewar ciwon zazzabi da ba'a gane irinsa ba a yankin Equateur, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 13, kuma daga cikin wasu mutane takwas da ke fama da zazzabin, an gano cewar, 2 daga cikin su suna dauke da kwayar cutar Ebola mai saurin kashe bil'adama.
Amma kuma ministan ya ce, a halin da ake ciki kasar ta samu nasarar dakilar da barkewar cutar ta Ebola a yankin Djera, a inda kuma ya yi kira ga al'ummar yankin da su kwantar da hankalinsu.
Ministan Lafiyar ya ce, kamuwar mutane biyu da aka gano a yankin ba ya da nasaba da barkewar cutar Ebola ta yankin Afrika ta yamma, wanda ya kawo ya zuwa yanzu ya haddasa mutuwar mutane sama da 1,400. (Suwaiba)