Rahotanni daga jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC na cewa, rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar MONUSCO, ta kaddamar da shirin ko-ta-kwana, domin yaki da yaduwar cutar Ebola, wadda aka hakikance ta bulla a kasar.
Da yake karin haske game da hakan, kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, bisa bayanan da suka fito daga ofishin kula da harkokin ba da agajin jin kai na OCHA, wannan cuta mai matukar hadari ta riga ta hallaka mutane 13, a garin Boende dake lardin Equateur mai nisan kilomita 1200 daga birnin Kinshasa.
Cikin ayyukan da MONUSCOn ke gudanarwa dai, akwai tantance lafiyar ma'aikatanta dake kaiwa da komowa a kasashen da Ebola ta riga ta bulla.
Dujarric ya kara da cewa, wannan shiri na MONUSCO kari ne, kan kokarin da hukumar WHO da hadin gwiwar kasar Congo, da ma sauran kungiyoyin sa kai ke yi don ganin sun dakile yaduwar ta.
An dai fara samun bullar cutar Ebola ne a janhuriyar dimokaradiyyar Congo a shekarar 1976, kuma bullarta a wannan karo ita ce 7 a tarihin kasar. Kaza lika kafin bullarta a bana, cutar ta hallaka mutane 36 a shekarar 2012, lokacin da ta bayyana a lardin Orientale. (Saminu)