in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitocin kasar Sin sun hada kai da 'yan uwansu na Afirka wajen yaki da cutar Ebola
2014-08-15 16:39:53 cri

A halin yanzu dai cutar Ebola tana kalubalantar kasashe da dama na yammacin Afirka, cutar da ta fi tsanani a tarihi tun bayan shekarar 1976 da aka fara ganon cutar Ebola, ya zuwa yanzu cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu. Game da bazuwar cutar Ebola, likitocin kasar Sin sun ci gaba da aiki tare da 'yan uwansu na Saliyo, kasar da ta fi shan wahalar cutar Ebola.

Shugaban tawagar likitoci da kasar Sin ta tura wa kasar Saliyo Mista Wang Yaoping ya gabatar da cewa, wannan tawagar da ke kunshe da likitoci 10 sun isa Saliyo ne a watan Afrilu na shekarar 2013, a halin yanzu dai sun riga sun shafe shekara guda suna aiki a asibitin gwamnati na Kong Harman Road da ke birnin Freetown, babban birnin kasar Saliyo. Ko da yake likitocin tawagar ba su da yawa, amma suna da cikakkun na'urori da fasaha wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

"Wannan asibiti da muke ciki yana karbar marasa lafiya dake fama da cututtuka daban daban a yankin Freetown, babban birnin kasar dalilin yawan jama'a, kuma muna da kayayyaki masu inganci, sakamakon haka jama'a masu yawan gaske suke zuwa wurinmu domin ganin likita. Muna da sassa daban daban kamar sashen da ke kula da lafiyar jiki, sashen kula da lafiyar mata, da na yara, da na idanu, da na kunne da dai sauransu, wani lokaci kuma muna gudanar da aikin tiyata da bincike ga mata masu ciki, sabo da haka muna gudanar da ayyukan kiwon lafiyar jama'a masu muhimmanci."

A hakika dai, sabo da bazuwar cutar Ebola cikin sauri, likitocin kasar Sin suna fuskantar manyan kalubaloli a fannonin ayyuka da zaman rayuwa. Game da haka, Mista Wang Yaoping ya ce,

"Bayan barkewar cutar Ebola, yawan majiyatta da suka zo asibitinmu ganin likita bai ragu ba, kuma wasu daga cikinsu kuma mai yiyuwa ne sun taba zuwa a yankunan da ake fama da cutar, kuma mutane daga wadannan yankunan da ke fama da cutar sun zo babban birnin kasar domin ganin likita, sakamakon haka ne ma, likitocinmu suna fuskantar kalubalen kamuwa da cutar Ebola. A hakika dai, a watan jiya, mun ga wani mutum, da kila ya kamu da cutar Ebola, nan da nan muka yi gwajin jininsa, rana mai zuwa kuma mun tabbatar da cewa, ya dauke da cutar Ebola. Irin haka ya kan kawo barazana ga likitocinmu."

Kara bazuwar cutar Ebola, ta sa wasu kasashe sun janye tawagogin likitocinsu zuwa gida, amma Mista Wang Yaoping ya ce, sabo da Sin da Afirka suna da dankon zumunci kamar 'yan uwa, kuma gwamnatin kasar Sin ta dorawa likitocinta nauyi mai girma, sabo da haka ne, likitocin kasar Sin za su ci gaba da hada kai da 'yan uwansu na Afirka wajen yaki da cutar Ebola. Mista Wang ya ce,

"Muna tsammanin cewa, dole ne mu gama aikinmu na ba da taimako ga Saliyo, da gwamnatin kasar ta dora mana, wannan kuma yana da nasaba sosai da aikinmu, wato ayyukan likitoci su ne ba da taimako ga marasa lafiya dake cikin barazanar mutuwa. Yayin da muke fuskantar manyan bala'u, tabbas ne likitoci su cigaba da bada taimako."

Ban da tawagar likitoci da ke karkashin shugabancin Mista Wang Yaoping, akwai wani asibiti sada zumunci a tsakanin Sin da Saliyo da ke da nisan kilomita 20 da Freetown, babban birnin kasar Saliyo, wanda a cikinsu likitocin kasar Sin su ma suna aiki tare da abokan aikinsu na wannan kasa. Mataimakin shugaban asibitin, wani likitan kasar Saliyo Dr. Kanu ya riga ya mayar da wadannan Sinawa a matsayin abokai tun da jimawa. Ya ce,

"Wadannan Sinawa abokanmu ne na gaskiya, sabo da haka ne ba su bar mu ba, sun ci gaba da taimaka mana. Ban yi tsammanin za su bar mu sabo da cutar Ebola ba. A ganina, za su ci gaba da aikin tare da mu."(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China