Da yake karin haske ga manema labaru a birnin Abuja, fadar gwamnatin kasar, Chukwu ya ce mutane biyun da aka hakikance sun harbu da Ebola iyalai ne ga dan Laberian nan da tun da fari ya shigar da cutar Najeriya.
Ya zuwa yanzu a cewar ministan akwai jimillar mutane 4 da aka kebe, sakamakon harbuwa da suka yi da cutar, yayin da kuma aka salami mutane 5 daga asibiti bayan da aka tabbatar sun warke sarai daga cutar.
Ministan ya kuma bayyyawa 'yan jaridun cewa gaba daya ana lura da mutane 213, domin gano ko suna dauke da Ebola, sakamakon mu'amala da ake zaton sun yi da wadanda suka harbu da cutar a baya. Kazalika ya ce gwamnatin Najeriya, da sauran kasashen duniya za su ci gaba da daukar matakan kandagariki, domin tabbatar da dakile yaduwar wannan cuta mai matukar hadari.
Daga nan sai ya godewa daukacin al'ummar Najeriya bisa gudummawar da suke baiwa mahukunta wajen yaki da yaduwar cutar ta Ebola. (Saminu Alhassan)