in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan kiwon lafiya 130 sun mutu sakamakon cutar Ebola
2014-08-25 10:55:13 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta tabbatar a ranar lahadi 24 ga wata cewa, a cikin watanni 6 da suka gabata, ma'aikatan kiwon lafiya a kalla 225 suka kamu da cutar Ebola, daga cikin su 130 sun mutu.

A wannan rana kuma, WHO ta tabbatar da cewa, wani ma'aikacin kiwon lafiya da hukumar ta tura wa Saliyo ya riga ya kamu da cutar Ebola. Wannan kuma ya zama karo na farko da ma'aikacin hukumar WHO ya kamu da wannan cutar.

WHO ta ci gaba da cewa, bisa tsarinta da kuma cibiyar sanar da barkewar cututtuka cikin gaggawa da tinkararsu ta duniya, an riga an tura ma'aikatan kiwon lafiya 400 zuwa ga Saliyo da Liberiya, da Nijeriya, da kuma Guinea domin taimaka musu wajen shawo kan cutar Ebola.

Bugu da kari, hukumar ta amince da cewa, wadannan ma'aikatan kiwon lafiya suna fuskantar kalubale a fannin lafiya, don haka, za ta dauki matakan rigakafi yadda ya kamata kafin a tura musu zuwa kasashen da ke fama da cutar Ebola. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China