MDD ta yi gargadi cewar, takunkumin haramcin shiga da fita kasashen dake fama da cutar Ebola a Afrika ta yamma yana iya kawo cikas wajen yaki da cutar Ebola mai saurin kisan bil'adama daga bangaren kasashen duniya.
Kakakin MDD, Stephane Dujarric ya bayyana cewar, haramcin da aka sa na hana jigilar jiragen sama na shiga da fita kasashen dake fama da cutar, da kuma kasashen da ake yin zango da kasashe makwabta suna kawo cikas wajen kokarin da MDD ke yi na yaki da cutar ta Ebola.
Dujarric ya ce, kasashen da suka haramta a shiga kasashensu su ma suna da hujja babba, to amma kuma kamar yadda ya ce, haramcin shige da fici da kasashen suka hana bai kamata ba, domin MDD ta mai da hankalinta wajen yaki da cutar.
To amma kasashe da dama wanda suka hada da Gabon, Senegal, Kamaru, Afrika ta Kudu da Rwanda sun yi watsi da kiran janye haramcin jigilar jiragen sama na shige da fici, kuma sun kakaba haramcin shiga kasashen dake fama da cutar ta Ebola. (Suwaiba)