Dokar ta kuma tanaji dauri a gidan maza da ka iya kaiwa har shekaru 2, ga duk wanda ya keta ta.
Kaza lika Mr. Kargbo ya shaida ta kafar watsa labarun kasar cewa, rabon da a samu bullar cutar ta Ebola a Saliyo tun shekarar 1960, ya zama wajibi a yanzu a yiwa tsohuwar dokar kiwon lafiyar kasa kwaskwarima.
Hukumar lafiya ta duniya WHO dai ta ce har ya zuwa yanzu, ba a kai ga fahimtar cikakken tasirin tsananin cutar Ebola a yammacin Afirka ba.
Hakan kuwa a cewar WHOn ya biyo bayan karancin fahimtar matakan shawo kan cutar, da tsoron da masu dauke da ita ke da shi na kebe su, bayan an tabbatar sun kamu da cutar. Hakan kuma ke sa wasu iyalai a wuraren da ake fama da yaduwar cutar Ebola boye 'yan uwansu masu fama da ita tare da musunta hakan. Har wa yau irin wadannan rukuni na jama'a kan binne gawawwakin wadanda suka rasu sakamakon cutar ba tare da sanar da ma'aikatan lafiya da masu aikin yaki da cututtuka ba. Don haka ba za a san dalilin mutuwar irin wadannan mutane ba.
Baya ga hakan, akwai kuma rashin gamsuwa da matakan da gwamnatoci ke dauka, da rashin motoci da sauran kayan aiki, wadanda ke haddasa yaduwar jita-jita a wasu wuraren masu fama da cutar ta Ebola, ta yadda har ya zuwa yanzu wasu garuruwa ko kauyukan dake fama da cutar, ba ma a san cikakken halin da suke ciki ba. (Maryam)