in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
• Ma'aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar Ebola mai tsanani 2014-08-26
Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta bayar da wani rahoto kan halin da ake ciki game da cutar nan mai matukar hadari ta Ebola, inda ta bayyana cewa, tun farkon barkewar cutar Ebola har zuwa yanzu, ma'aikatan kiwon lafiya 240 ne suka kamu da cutar, inda rabinsu suka mutu. WHO na ganin a wannan karo ma'aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar ta Ebola mai tsanani, wanda ba a taba ganin irinta a baya ba...
• Jama'ar Afirka suna da bambancin ra'ayi game da amfani da magungunan gwaji kan cutar Ebola  2014-08-20
A 'yan kwanakin baya, hukumar lafiya ta duniya WHO ta yarda da yin amfani da magungunan gwaji wajen shawo kan cutar Ebola, bayan haka kuma, kasashen Amurka da Canada da dai sauransu bi da bi suka baiwa kasashen na Afirka wadannan magunguna a karo na farko, amma jama'ar nahiyar Afirka sun nuna bambacin ra'ayi game da amfani da wadannan magunguna...
• Kungiyar SADC ta bukaci mambobinta da su mai da hankali kan rigakafin cutar Ebola  2014-08-19
An rufe taron shugabannin kungiyar raya yankin kasashen kudancin Afirka wato SADC karo na 34, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a birnin Victoria Falls da ke kasar Zimbabwe, inda kungiyar ta bukaci mambobinta da su mai da hankali kan rigakafin cutar Ebola, a karshen taron mambobin kungiyar sun cimma ra'ayi guda don ganin wannan yanki ya kasance tamkar tsintsiya madaurin ki daya...
• Yadda za ka wanke hannunka domin yaki da cutar Ebola 2014-08-15
Idan har ba ka wanke hannunka yadda ya kamata ba sannan ka taba fuskarka ko wuraren da jama'a ke amfani da su, hakika kana iya kamuwa da kwayoyin cuta har ma ka yada wa wasu kamar cutar zawo da mura, dukkansu ana yada su ne idan mutum ya taba hannun wani...
• Likitocin kasar Sin sun hada kai da 'yan uwansu na Afirka wajen yaki da cutar Ebola 2014-08-15
A halin yanzu dai cutar Ebola tana kalubalantar kasashe da dama na yammacin Afirka, cutar da ta fi tsanani a tarihi tun bayan shekarar 1976 da aka fara ganon cutar Ebola, ya zuwa yanzu cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu. Game da bazuwar cutar Ebola, likitocin kasar Sin sun ci gaba da aiki tare da 'yan uwansu na Saliyo, kasar da ta fi shan wahalar cutar Ebola...
• Kasar Sin ta taimakawa kasar Saliyo wajen yaki da cutar Ebola 2014-08-14
A halin da ake ciki cutar Ebola tana kara yaduwa a kasashe da dama da ke yammacin Afirka, cutar da tuni ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu. A cikin wannan hali ne gwamnatin kasar Sin ta yi jigilar kayayyakin jin kai cikin gaggawa, ta kuma aike da kwararru a fannin kiwon lafiyar jama'a 9 zuwa kasashen Guinea, da Saliyo, da Liberiya, kasashen da suka fi fama da wannan cutar. Game da haka, mataimakiyar ministan harkokin wajen Saliyo Madam Ebun Strasser-King, ta bayyanawa mahalarta bikin karbar kayayyakin cewa, gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar tallafi a wannan mawuyacin halin da ake ciki, wanda gwamnati da jama'arta ba za su manta da shi ba...
• WHO ta yarda da amfani da magungunan gwaje-gwaje kan cutar Ebola 2014-08-13
Ganin yadda annobar Ebolo ta barke cikin sauri a yammacin Afirka, da yadda har zuwa yanzu ba a samu magungunan musamman na allurar rigakafin cutar ba. Game da haka, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta kira wani taro da ya kunshi kwararru 12 da suka fito daga kasashe daban daban, domin tattauna yiwuwar ganin ko za'a dace da ka'idojin likitanci ko a'a wajen yin amfani da magungunan gwaje-gwaje kan cutar Ebola. Mai ba da taimako ga babbar sakatariyar hukumar WHO Madam Marie-Paule Kieny ta bayyana a gun taron manema labaru cewa...
• Nijeriya ta tsaurara matakan tinkarar Ebola 2014-08-12
Baya ga kasashen Guinea da Liberia da Saliyo, Nijeriya ta zama kasa ta hudu a nahiyar Afirka da aka gano bullar cutar Ebola, inda ya zuwa ranar 11 ga wata aka tabbatar da mutane 10 da suka kamu da cutar. Abokiyar aikinmu Lubabatu na dauke da karin bayani...
• Kasar Sin na kokarin tallafawa kasashe uku na yammacin Afirka wajen yaki da cutar Ebola 2014-08-11
Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya wato WHO, ta bayar da sanarwa a ranar 8 ga wata a birnin Geneva, cewa yaduwar cutar Ebola ta zama wani lamarin kiwon lafiya na gaggawa dake jawo hankulan kasashen duniya. Ka na ta yi kira ga kasashen duniya da su ba da taimako ga kasashen yammacin Afirka dake fama da wannan cuta. Har wa yau a dai wannan rana, gwamnatin kasar Sin ta tashi wani jirgin sama mai dauke da kayayyakin aikin jinya har Ton sama da 80, wanda a yanzu haka ke kan hanyar sa zuwa kasashen da cutar ta fi shafa...
• Matsalolin da ake fuskanta wajen shawo kan cutar Ebola  2014-08-04
Cutar Ebola da ake fama da ita a yanzu haka a yammacin Afirka ya ta jawo hankalin duniya baki daya. Ahakika, ann fara gano cutar ne ce tuni a shekarar 1976, amma me ya sa a cikin tsawon kusan shekaru 40 da suka wuce, babu wata hanyar da aka gano ta shawo kan cutar, shin wadanne wahalhalu matsaloli ne ake fuskanta wajen tunkarar wannan cuta? Abokiyar aikinmu Lubabatu na tare da karin bayani...
• Bai kamata Sinawa su damu da cutar Ebola ba, in ji kakakin WHO 2014-07-31
Kakakin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Paul Garwood ya bayyana a ranar talata 30 ga wata cewa, ko da yake wadansu kasashe a nahiyar Afrika na fama da cutar Ebola, bai kamata Sinawa su damu game da hakan ba saboda ganin wata 'yar yankin Hongkong ta kamu da cutar bayan data dawo daga nahiyar Afirka...
• Ya kamata a yi taka tsantsan a kan Ebola, in ji WHO 2014-04-09
A ranar 8 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta duniya(WHO) da ke da hedkwatarta a birnin Geneva ta bayyana cewa, cutar Ebola da ake fama da ita a yanzu haka a yammacin Afirka na daya daga cikin cututtukan da suka fi kawo kalubale tun lokacin da aka fara gano ta, abin da ya kamata a yi taka tsantsan a kai...
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China