in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar SADC ta bukaci mambobinta da su mai da hankali kan rigakafin cutar Ebola
2014-08-19 15:21:19 cri

An rufe taron shugabannin kungiyar raya yankin kasashen kudancin Afirka wato SADC karo na 34, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a birnin Victoria Falls da ke kasar Zimbabwe, inda kungiyar ta bukaci mambobinta da su mai da hankali kan rigakafin cutar Ebola, a karshen taron mambobin kungiyar sun cimma ra'ayi guda don ganin wannan yanki ya kasance tamkar tsintsiya madaurin ki daya.

Ko da yake babu mutanen da suka kamu da cutar Ebola a kudancin Afirka a halin yanzu, amma kasashen da ke wannan yanki sun riga sun dauki matakan da suka dace na yin rigakafin cutar. A sanarwar bayan taron da shugabannin kungiyar SADC suka fitar a wannan karo, an bukaci mambobinta su dauki ingantattun matakai domin shawo kan cutar ta Ebola. Sakatariyar zartaswar kungiyar SADC Madam Stergomena Tax ta bayyana cewa,

"A yayin wannan taro, an tantance irin kalubalen da ake fuskanta sanadiyyar cutar Ebola. Kungiyar SADC ta bukaci kasashe mambobinta da su ci gaba da ba da muhimmanci matuka kan matakan kandagarkin cutar ta Ebola, domin ya zama tilas a magance ta da zarar an gano bullar cutar a kudancin Afirka."

Manufar wannan kungiya ta Afirka mai kasashe mambobi 15 wato SADC, ita ce raya tattalin arzikin yanki bai daya. A gun taron shugabannin kungiyar na wannan karo, mambobin kungiyar sun daddale wasu yarjejeniyoyi domin kara hada kansu. Kungiyar ta kuma yi nuni da cewa, za ta fi bayar da muhimmanci ga aikin raya masana'antun kasashen dake yankin. Shugaban SADC na wannan karo, kana shugaban kasar Zimbabwe Mista Robert Mugabe ya bayyana bukatar kafa wani asusun na raya yanki. Ya ce,

"Muna mai da hankali kan ci gaban da aka samu wajen kafa asusun raya yankinmu. Kafuwar asusun, za ta samar mana kwarewa wajen zuba jari a kasashenmu, da aiwatar da ayyukan a cikin yankinmu, da rage dogaro fiye da kima kan kasashen waje."

A 'yan shekarun baya, kungiyar SADC ta aiwatar da wasu shirye-shiryen siyasa da tsaro a yankunansu. Kungiyar SADC ta kuma yi kokari tare da sauran kasashen duniya, inda suka yi shiga tsakani kan halin da ake ciki a gabashin Kongo(Kinshasa), da sa kaimi ga Madagascar da Zimbabwe da su daidaita ricikin siyasa da suke fuskanta a kasashen. Jakadan kasar Sin da ke kasar Botsowana kuma wakilin kasar Sin da ke kungiyar SADC, wanda aka gayyata a taron na shugabannin kungiyar SADC na wannan karo, Mista Zheng Zhuqiang ya bayyana cewa, kungiyoyin shiyya-shiyya kamar SADC, suna taka wata muhimmiyar rawa wajen shimfida zaman lafiya da na karko a nahiyar Afirka.

"Al'ummar Afirka suna kula da harkokinsu da kansu, wannan wani abu ne mai kyau. Wannan zai taimaka wajen kara shimfida zaman lafiya har ma da kyautata makomar Afirka, wannan shi ne burin al'ummomi da jam'iyyun siyasa na Afirka."

A gun taron shugabannin SADC na wannan karo, an zabi sabbin shugabannin wasu hukumomin kungiyar, inda shugaban kasar Afirka ta Kudu Mista Zuma shi aka zaba a matsayin shugaban hukumar da ke kula da harkokin siyasa da tsaro na SADC. Bisa labarin da muka samu, an ce, za a shirya taron shugabannin kungiyar na shekarar 2015 a kasar Botsowana. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China