Wata guda kacal bayan taron shawarwari na farko domin fuskantar annobar cutar Ebola, ministocin kiwon lafiya na kungiyar cigaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) za su sake shirya wani sabon taro a ranar Alhamis mai zuwa domin tattauna matakan yaki da cutar Ebola da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu daya da dari hudu tun daga cikin watan Febrairu. Wannan taron gaggawa zai biyon bayan wani taron kwararrun kiwon lafiya na tsawon kwanaki biyu wato a ranakun Laraba da Alhamis, a cewar wata sanarwar ma'aikatar kiwon lafitar kasar Ghana. (Maman Ada)