in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a samu fahimtar tsananin tasirin cutar Ebola ba, in ji kungiyar WHO
2014-08-23 16:44:55 cri
Jiya Jumma'a 22 ga wata, kungiyar kiwon lafiya ta WHO ta ba da sanarwar cewa, har yanzu ba a samu cikakkiyar fahimtar tasirin tsananin cutar Ebola a yammacin Afirka ba tukuna.

Kungiyar WHO ta ce, dalilin rashin fahimtar matakan shawo kan cutar Ebola, da jin tsoron za a kebe su zuwa wuri daban bayan tabbatar da kamuwa da cutar, wasu iyalai a wuraren dake fama da cutar Ebola sun boye 'yan uwansu dake famamasu kamu da cutar tare da musunta hakan, ko sun bene binne gawawwaki ba tare da sanar da ma'aikatan lafiya da yaki da cututtuka, wadanda kumaduk da cewa ba a san dalilin mutuwarsu mutanen ba. Bayan haka, rashin amincewa da matakan da gwamnati ta dauka, da rashin motoci da sauransu, sun haddasa yaduwar jita-jita a wasu wuraren dake fama da cutar Ebola, har ma wasu garuruwa kauyuka dake fama da cutar, ba a san cikin ainihin halin da suke ciki ba har zuwa yanzu.

Kungiyar WHO ta ce, yanzu cutar Ebola dake yaduwa ta zama babban kalubale ga kokarin shawo kan cutar. Yanzu a yammacin Afirka yYawan ma'aikatan ba da jiyya, da hidimomin ba da jiyyada ake samar, da kayayyakin likitanci da sauransu dukkansu ba za su iya biyan bukata ba tukuna.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China