in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar Ebola mai tsanani
2014-08-26 16:03:40 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta bayar da wani rahoto kan halin da ake ciki game da cutar nan mai matukar hadari ta Ebola, inda ta bayyana cewa, tun farkon barkewar cutar Ebola har zuwa yanzu, ma'aikatan kiwon lafiya 240 ne suka kamu da cutar, inda rabinsu suka mutu. WHO na ganin a wannan karo ma'aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar ta Ebola mai tsanani, wanda ba a taba ganin irinta a baya ba.

Kasashe hudu da ke yammacin Afirka inda cutar Ebola ta fi tsananta wato Guinea, da Liberiya, da Saliyo da kuma Nijeriya, dukkan su na fuskantar karancin bunkasuwar rayuwar al'ummun su, inda daga cikin wadannan kasashen wasu suka shafi shekaru da dama suna fama da rikice-rikice, ban da karancin tsarin kiwon lafiya mai inganci, irin wadannan kasashe na kuma fama da karancin isassun ma'aikatan kiwon lafiya.

Game da bazuwar cutar Ebola ba zato ba tsammani kuwa, tsarin kiwon lafiyarsu ba ya da kwarewar shawo kan cutar. A wannan halin da ake ciki, WHO ke jan hankalin ma'aikatan kiwon lafiya na duniya game da kaiwa wannan yanki dauki.

Kakakin WHO Mista Tarik Jasarevic ya bayyana cewa,

"Lallai kada mu manta, wannan ne karo na farko da kasashen da ke yammacin Afirka suke fuskantar yaduwar cutar Ebola cikin saurin kwarai, a sa'i daya kuma, ba su da tsarin kiwon lafiya mai inganci, kuma ba su da isassun ma'aikatan kiwon lafiya. Sabo da haka ne, cutar Ebola a wannan karo ta haifar da babbar illa ga tsarin kiwon lafiyar su. Sakamakon hakan ne kuma ya sa ake bukatar tura ma'aikatan kiwon lafiya na sauran yankuna zuwa yammacin Afirka a daidai wannan mawuyacin hali da ake ciki."

Rahoton da WHO ta fitar ya yi nuni da cewa, wasu daga ma'aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar Ebola mai tsanani, irin wadda ba a taba ganin irinta ba a baya.

Game da hakan Mista Tarik Jasarevic ya bayyana cewa, hanyar da cutar Ebola take bi wajen yaduwa, ta zama wani babban dalilin da ya sanya ma'aikatan kiwon lafiyar kamuwa da ita. Ya ce,

"Yayin bullar cutar Ebola ta wannan karo mun gano cewa, ma'aikatan kiwon lafiya na cikin rukunin jama'ar da suka fi kamuwa da ita. Sabo da yawan mu'ammalar da suke yi da majiyatta kai tsaye, duba da cewa cutar Ebola, ta kan yadu ta ruwan jikin majiyatta. Tun daga farkon barkewar cutar Ebola har zuwa yanzu, ma'aikatan kiwon lafiya 240 ne aka hakikance sun kamu da cutar, kana rabinsu sun riga sun rasu."

Bugu da kari hukumar ta WHO ta yi tsokaci game da sauran dalilan da ke haddasa yaduwar cutar Ebola. Kamar batun rashin iya samar da isassun kayayyakin kandagarkin ta, ko gaza amfani da su yadda ya kamata, da kuma babu isassun ma'aikatan kiwon lafiya, sabo da haka wasu daga kalilan na ma'aikatan lafiyar kan gudanar da ayyuka fiye da kwarewarsu, ko ikon da suke da shi. WHO ya yi nuni da cewa, lallai wadannan wahalolin da ma'aikatan kiwon lafiya ke fuskanta na kawo babbar illa ga matakan da ake dauka wajen shawo kan yaduwar cutar Ebola.

A halin yanzu dai, WHO da abokan aikinta sun riga sun dauki wasu matakai na kandagarki ga ma'aikatan kiwon lafiya da za a tura zuwa yankunan da ke fama da yaduwar cutar ta Ebola. Bayan isar su wadannan yankuna, za su ba da jagoranci da horaswa ga takwarorinsu dake yankunan.

Baya ga hakan, WHO ta bukaci da a samar da kayayyaki irin wadanda za su dace da yankunan da ake tura su, su kuma dace da ma'aunin tsaro na duniya. Ban da wannan, kungiyar tarayya kasashen Afirka ta AU ta gabatar da wata shawarar kara samar da ma'aikatan kiwon lafiya daga kasashe mambobinta.

Bisa kiyasin da wasu kwararru suka yi, an ce, a kalla za a shafe rabin shekara ana kokari, kafin shawo kan halin da ake ciki na yaduwar wannan cuta ta Ebola. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China