in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar Afirka suna da bambancin ra'ayi game da amfani da magungunan gwaji kan cutar Ebola
2014-08-20 16:44:40 cri

A 'yan kwanakin baya, hukumar lafiya ta duniya WHO ta yarda da yin amfani da magungunan gwaji wajen shawo kan cutar Ebola, bayan haka kuma, kasashen Amurka da Canada da dai sauransu bi da bi suka baiwa kasashen na Afirka wadannan magunguna a karo na farko, amma jama'ar nahiyar Afirka sun nuna bambacin ra'ayi game da amfani da wadannan magunguna.

A ranar 13 ga wata ne, ministan harkokin wajen kasar Liberiya ya yi jigilar akwatuna biyu na magungunan gwajin cutar ta Ebola daga Amurka ta jirgin sama, domin warkar da likitoci biyu na kasar wadanda suka kamu da cutar ta Ebola, a sa'i daya kuma, ministan kiwon lafiya na kasar Canada ya sanar da cewa, kasarsa za ta baiwa Afirka kyauta allurai kimanin dubu daya, wasu masana'antun harhada magunguna sun bayyana cewa, za su iya hada allurai fiye da dubu 10 a cikin watanni 1 ko 2 masu zuwa.

A kasar Nijeriya da cutar Ebola ke bazuwa, Madam Kemi da ke aiki a wani kamfanin intanet na birnin Abuja, babban birnin kasar, ta yi nuni da cewa, ko da yake ba a san ko za a iya samun nasara wajen warkar da wadanda suka kamu da cutar ko a'a, amma a ganinta, mutanen da suka kamu da cutar Ebola suna son karbar magungunan gwajin.

"Idan na kamu da cutar Ebola, zan karbi maganin gwajin, idan ban yi haka ba, watakila zan mutu, amma idan na sha maganin, watakila zai taimaka, ko da yake amfanin da maganin zai yi kadan, duk da haka motsi ya fi labewa ,saboda haka a gani ba wanda zai ki karbar maganin."

Wani mazaunin Abuja,mai suna Malam Audu Ujoh yana da bambancin ra'ayi, a ganinsa, ba zai sha maganin ba duk da cewa, zai mutu. Ya ce,

"Ba zan yi amfani da wannan magani ba, sabo da ban yi imani da maganin da ba a taba yin gwaji a kansa ba, idan na sha maganin, mai yiyuwa ne zai halaka ni, domin ba san irin illar da maganin zai yi mini, ba zan sha maganin ba na fi son na mutu maimakon na shan wannan magani."

Mamban hukumar likitanci ta ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Nijeriya, kuma babban likita a asibitin MFM na birnin Abuja Mista Onyoh ya shaida wa manema labarai cewa, ko da yake cutar Ebola cuta ce ma fi illa a duk duniya, amma wasu mutane ba su mutu sakamakon cutar ba, wannan ya sa wasu matakan kariyar da ke jikin wasu mutane suna iya haifar da kwayoyin da ke yakar da Ebola, Wasu Amurkawa biyu da suka samu sauki ta bayan da aka sanya musu kwayoyin da ke yakar cutar a cikin jikinsu, wannan ya kara sanya shakku ga jama'a kan amfani da sabon magungunan gwajin da ke shawo kan cutar ta Ebola. Ya ce,

"Wani abin lura shi ne, kafin a kai su a Amurka daga Liberiya, likitocin Amurka sun samu kwayoyin yakar Ebola daga jinin mutanen da suka warkar daga cutar ta Ebola, sa'an nan kuma aka shigar da kwayoyin yakar cutar jikin Amurkawan biyu, bayan da suka koma Amurka, wadannan Amurkawa sun sake samun jinya ta hanyar shan wani sabon maganin gwajin, daga bisani kuma sun samu sauki, amma wani likitan Spain da ya mutu, ko da yake ya sha sabon maganin gwaji, amma ba a sanya masa kwayoyin yakar cutar ta Ebola a jikinsa ba."

A ganin Mista Onyoh, matakin da ya fi dace wa a halin yanzu shi ne a yi rigakafi da shawo kanta yayin da aka kamu da cutar Ebola nan da nan. Ya ce,

"Amfanin magani shi ne warkar da mutanen da suka kamu da cutar Ebola, amma a ganina wani abu mai muhimmanci shi ne, a yi rigakafi tare da shawo kan yayin da aka kamu da cutar nan da nan. Tilas ne a binciki yanayin zafin jikin jama'a sosai a filayen jiragen sama, da kan iyaka, domin tabbatar da cewa an kebe mutanen da suka kamu da cutar Ebola, Yanzu mutanen da ake shakkun sun kamu da cutar da wadanda aka tabbatar cewa sun kamu da cutar,dukkan su sun taba yin cudanya da mutumin da ya kamu da cutar na farko daga kasashen waje, idan ban da birnin Lagos, ba a gano sabbin wadanda suka kamu da cutar ba, a hakika dai an riga an dakile yaduwar cutar ta Ebola a kasar ta Najeriya." (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China