A cewar Mr. Sano a yanzu haka kasar ta Guinea na amfani da kayayyakin agajin kasar ta Sin, wajen gudanar da ayyukan jinya ga wadanda aka tabbatar da cewa suka kamu da cutar, kana kayayyakin sun taimaka wa ma'aikatan jinya wajen hana kamu da cutar.
Bugu da kari a cewar ministan har bayan kaiwa ga karshen yaduwar cutar ta Ebola a wannan karo, za a iya ci gaba da amfani da wadannan kayayyakin agaji.
Daga nan sai Sano ya gabatar da matukar godiyar kasarsa ga mahukuntan kasar Sin bisa wannan taimako, musamman a wannan lokaci da Guinea ke cikin matukar bukatarsa, a kuma gabar da wasu kasashen ba su samar da wani tallafi makamancin wannan ba.
Sano ya kara da cewa wannan taimako na kasar Sin na da muhimmiyar ma'ana ga al'ummomin kasarsa, ya kuma nuna kasancewar kyakkyawar dangantakar sada zumunci mai zurfi tsakanin jama'ar kasashen biyu. (Maryam)