A wannan rana, a gun taron manema labaru da aka shirya a hedkwatar MDD dake birnin New York, mista Dujarric ya bayyana cewa, kungiyar WHO tana kokarin fitar da wani shiri da zai shafi watanni 6 zuwa 9, domin shawo kan cutar Ebola. Ya ce, wannan ne wani shirin aiki, inda za a gabatar da cikakkun matakan da za a dauka wajen yaki da cutar. An kiyasta cewa, za a fitar da shi a farkon mako mai zuwa.
Bayan haka, mista Dujarric ya kara da cewa, game da shawarar da wasu kasashe suka yanke a kwanan baya cewa, za a hana masu bulaguro daga kasashen dake fama da cutar Ebola zuwa wadannan kasashe, kungiyar WHO ta jaddada cewa, bai kamata ba a so fitar da umurnin hana yawon shakatawa ko yin cinikayya a sakamakon haka. Dalilin da ya sa haka shi ne, wannan ba zai hana yaduwar cutar Ebola ba, har ma zai kawo babbar illa. Kuma hakan zai iyar haifar da matsalar jin kai a wadannan kasashen dake fama da cutar Ebola, kuma zai kafa shinge ga kokarin sauran kasashen duniya na shawo kan cutar Ebola.
Bayan haka, mista Dujarric ya bayyana cewa, babban mai shiga tsakani kan cutar Ebola na MDD, David Nabarro ya yi shawarwari da wasu jami'an kiwon lafiya na Liberia a wannan rana, tare da kai ziyara a wani asibiti dake birnin Monrovia, hedkwatar kasar.(Fatima)