Kasar Rwanda ta sanar da dokar dakatar da 'yan kasarta tafiya zuwa kasashe masu fama da cutar Ebola, kamar yadda ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bayyana cikin wata sanarwa a Litinin din nan.
Wannan mataki dai ya biyo bayan sabon rahoton dake nuna bullar cutar a makwabciyar ta jamhuriyar demokuradiyar Congo, abin da ya nuna yadda cutar ke saurin yaduwa.
Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta jaddada cewa, duk wani matafiyi da ya fito ko zai shiga kasashen jamhuriyar Guinea-Conakry, Liberiya da Saliyo a cikin ranaiku 22, za'a dakatar da shi domin mashi gwajin jikin shi kafin ya shigo kasar Rwanda, ko kuma fita ta ko wace hanyar sufuri. Sai dai kuma wanda har ya samu wasikar izini ta musamman daga wajen ministan kiwon lafiyar kasar ta Rwanda, in ji sanarwar.
Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar dai ta tabbatar da tsaurara matakan sa ido a cikin al'umma da kuma duk wassu hanyoyi na shigowa kasar da suka hada da kan iyakokin kasar da filin saukar jiragen sama.
MDD dai ta riga ta soki wannan mataki da Rwanda ta dauka a kan zuwa kasashe masu fama da cutar Ebola, sai dai kasashe da dama sun riga sun dauki wannan mataki da suka hada da Ivory Coast, Senegal, Kamaru, Gabon da kuma Afrika ta Kudu. (Fatimah)